Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya karbi katin shiga sabuwar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP.)
Dubban magoya bayan Shekarau ne suka yi tururawa zuwa unguwar Mundubawa a birnin Kano, inda gidan tsohon gwamnan yake domin shaida bikin karbar katin jam’iyyar mai alamar kayan marmari.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya mikawa Shekarau katin jam'iyyar, kamar yadda rahotannin suka nuna.
Kwankwaso shi ne jagoran sabuwar jam’iyyar ta NNPP, wacce aka kafa a ‘yan watannin bayan nan, inda zai yi takarar shugaban kasa karkashinta.
“An gama wasan! Maraba da zuwa jam’iyyar NNPP Sanata Ibrahim Shekarau.” Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar ta NNPP Abdulmumin Jibrin ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Sanata Shekarau wanda ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa, ya shiga majalisar ne karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasa,
Sai dai rikicin cikin gida da jam’iyyar ta yi ta fuskanta, ya sa tsohon ministan ilimin ya koma NNPP.
Dama dai an yi ta rade-radin cewa Shekarau zai bar jam’iyyar ta APC, inda har a wasu lokuta ma wasu rahotanni suka nuna yana musantawa, amma daga karshe al’amura suka sauya.
Masu lura da al’amuran siyasa a jihar ta Kano, wacce ke da miliyoyin masu kada kuri’a, sun yi nuni da cewa, wannan wani babban kamu ne da jam’iyyar ta NNPP ta yi da ka iya yin tasiri a zaben 2023 da ke karatowa.