An sanar da mutuwar Adi mai shekaru 61 da haihuwa, wanda ya rasu bayan gajeriyar jinya, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannu kakakin jam’iyyar LP na kasa, Abayomi Arabambi, inda aka ambaci ta bakin shugaban jam’iyyar na kasa Julius Abure.
Abure ya bayyana rasuwar Adi a matsayin abin mamaki, yana mai cewa tabbas za’a yi kewar irin gudumuwar da zai iya bayarwa wajen zaben gwamnatin jama’a.
Ya ce “Jam’iyyar ta nuna matukar alhininta kan mutuwar Shirsha Adi, wanda aka bayyana a matsayin “mutum ne mai kwazo da jajircewa da ya bayar da gudumuwa matuka gaya wajen ci gaban jam’iyyar a shiyyar,” sannan ya bukaci iyalan mamacin da su jure wannan rashi tare da nuna cewa Allah masani.
Bisa ga cewar Shugaban jam’iyyar, “Wannan ba irin labaran da muke sa ran yadawa ba ne. Amma a matsayinmu na masu Imani, ba zamu tambayi Allah ba, Shi ne mafi sani.”
“A matsayinmu na masu Imani, ba mu da wani zabi illa mu godewa Allah a kan rayuwarsa. Kuma a matsayinmu na jam’iyya, zamu ci gaba da samun cigaba a falsafar da yake fata.”
Jam’iyyar ta bukaci iyalansa da su ci gaba da dorawa kan kyawawan ayyukan da mahaifinsu ya bari
Adi ya fito daga karamar hukumar Konshishi ta jihar Benue, kuma ya bar mata da ‘ya’ya uku.