ZABEN 2023: Tarihin Rabiu Musa Kwankwaso Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar NNPP

Rabiu Kwankwaso (NNPP)

An haifi Mohammed Rabiu Musa da akafi sani da Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 67 da suka shude a garin Kwankwaso na karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano Najeriya.

Ya halarci karamar makarantar firamare ta Kwankwaso da babbar firamare a garin Gwarzo. Sai makarantar koyon sana’o’i ta Wudil kana daga bisani ya wuce kwalejin koyon sana’o’i da kere-kere ta Kano wato Technical College Kano, inda bayan kammalawa ya tafi kwalejin fasaha ta Kaduna, inda ya samu karama da babbar Diploma.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala karatun Digiri na biyu akan fasahar injiniyan samar da ruwa a Jami’ar Lougborough da ke kasar Burtaniya a shekarar 1985, kana a bara ya kammala karatun digiri na uku wato Ph’D a Jami’ar Sharda ta kasar Indiya.

Yayi aiki a kamfanin WRECCA mai aikace-aikacen gina madatsun ruwa da hanyoyin mota mallakar gwamnatin Kano tsawon shekaru 17, kana daga bisani ya shiga harkokin siyasa a shekarar 1991, har ma ya zama dan majalisar wakilai ta Najeriya, inda aka zabe shi mataimakin shugaban majalisar.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Bayan rushewar majalisar a shekarar 1993, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya zama wakili a zauren babban taron kasa na sauya fasalin kundin tsarin mulki a shekarar 1995 a zamanin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Hon. Habibu Hassan Elyakub, tsohon dan majalisar dokokin Kano ne, kuma sun fito lardi daya da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kwankwanso tun yana yaro akwai alamun nutsuwa a tare dashi, kuma mutum ne mai son alkinta kudi da abin da ya mallaka.

A shekarar 1999 ne aka zabi Dr Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin gwamnan Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP bayan da Najeriya ta dawo tafarkin dimokaradiyya, kuma ya ja ragamar gwamnatin Kano tsawon shekaru hudu.

Hon. Isyaku Ibrahim Kunya, daya daga cikin hadiman gwamnan da suka yi aiki kud-da-kud a gidan gwamnati, ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na da hangen nesa a sha’anin shugabanci da tafiyar da harkokin gwamnati, hakan ta sanya ya sami damar kirkiro da sabbin abubuwa da zasu ciyar da rayuwar al’umma gaba, musamman a fannin ilimi tun daga tushe.

Senator Rabiu Musa Kwankwaso.

Gabanin ya zama gwamna, tun yana ma’aikacin gwamnati, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya fara nuna kishin al’umar yankin daya fito, a cewar Hon Habib Hassan Elyakub.

“A lokacin ni ina ma’aikatar ilimi shi kuma yana kamfanin WRECCA mallakar gwamnatin Kano, mun kafa kungiyar dalibai da ma’aikata ‘yan asalin yankin hayin Kogi, a lokacin muna karkashin gundumar Rano, saboda da ma mu lardinmu yana fuskantar kalubalen ababen more rayuwa, hakan ta sanya muka kafa wannan kungiya kuma shi ne ya shugabance ta, inda muka yi nasarar shiga gaba wajen samar da abubuwa a fannin ilimi da lafiya a garuruwanmu da kauyuka,” a cewar Elyakub.

Masu kula da lamuran mulki da harkokin dimokaradiyya a Kano sun lura cewa, an sami bambanci kan yadda Kwankwaso ya gudanar da gwamnatinsa ta farko da ta biyu a jihar Kano.

To amma Hon Isyaku Ibrahim Kunya ya fayyace dalilan hakan yana mai cewa watakila maganar wannan bambanci ba zata rasa nasaba da yadda a lokacin gwamnati ta farko wasu mutane suka rinka kokarin kawo wa gwamnati cikas ba, kuma dole ne da ya samu gwamnati a karo na biyu ya koyi darasi, domin kada ya maimaita kuskuren daya faru a baya.”

A yanzu dai Dr Rabiu Musa Kwankwaso na cikin jerin mutanen da ke takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar NNPP a zaben da za a yi yau Asabar, kuma Hon. Umar Haruna Doguwa, shugaban reshen jihar Kano na Jam’iyyar ya yi karin haske akan dalilan Kwankwaso na yin wannan takara.

Tsohon gwamnan Kano, Dr Rabiu Musa Kwankwaso

"Yana da gogewa a bangarori da yawa, ya yi aikin gwamnati, ya zama gwamna, ya yi minista kuma ya yi dan majalisar dokokin Najeriya a lokuta dabamdaban, wannan ya sa ya ke da sanin makama, kuma gashi da kishin Najeriya da mutanenta, don haka muke ganin idan ya zama shugaban kasa zai fitar da Najeriya daga halin da take ciki”.

Daga lokacin da ya zama gwamnan Kano a shekarar 1999 zuwa yanzu da ya ke neman ya zama shugaban Najeriya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magoya baya da daliban siyasa da dama, koda yake wasu daga cikinsu ba sa tare a yanzu.

Alhaji Umar Labaran Danga, mai lakabin Shehin Kwankwasiyya, na daga cikin tsaffin daliban Kwankwaso na kud-da-kud a siyasa. Ya ce Dr Rabiu Musa Kwankwaso mutum ne mai jajircewa akan abin da ya sanya a gaba, zai koya maka siyasa muddin kana tare dashi ba tare da bambanci ba, kuma mutum ne mai kokarin kiyaye karya, inda ya yi alkawari yana kokarin ya cikawa. Amma raunin sa shi ne mutum ne wanda bai faye karbar shawara ba, yana da son kansa, baya so ya ga wani ya fi shi, yana son kowa ya zama a karkashinsa, kowa ya zama yaronsa," a cewar Danga.

Dr Rabiu Musa Kwankwaso wanda yanzu haka ke da mata daya da ‘yaya, a baya-bayan nan ya ziyarci cibiyar Chartham House da ke birnin London, inda ya kara nanata manofofi da tsare-tsaren da zai aiwatar muddin ya zama shugaban Najeriya.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

KWANKWASO’s PROFILE.mp3