Yayin da ake cigaba da samun Karin 'yan takara dake neman kujerar shugabancin Najeriya a babban zaben kasar da ke tafe a shekarar 2023, Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sani Yariman Bakura ya shiga jerin wadanda suka aiyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Tsohon gwamnan ya jagoranci taro na musamman don ayyana niyyar takarar ta shi, wacce ta biyo bayan wata ganawa da ya yi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Juma’a a garin Abuja.
Tun a zaben 2019, Sani Yarima ke cewa zai yi takara matukar shugaba Buhari ba zai tsaya ba, ga shi yanzu shugaban na shirin kammala wa’adinsa na karshe ne na mulki.
Sani Yarima ya ce idan in an zabe shi zai yi kokarin inganta abubuwa uku wadanda suka hada da lamuran tsaro, talauci da kuma jahilci, batun da a cewarsa idan aka mai da hankali akansu Najeriya za ta samu kwaciyar hankali.
Ku Duba Wannan Ma Zaben 2023: Masu Ruwa Da Tsaki Na Nuna Shakku A Zabukan Tsaida Yan TakaraA gefe guda shi ma tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya, Dimeji Bankole, ya shiga jerin masu son takarar a APC.
Tsohon gwamnan Zamfara Mahmud Shinkafi ya jagoranci tawagar da ta saya wa Bankole fom din takara Naira miliyan 100.
Ba za a yi mamaki ba in masu takara a APC kadai za su iya kai wa mutum 30 kafin rufe sayar da takardun takarar.
Saurari hirar da shamsiyya Hamza Ibrahim ta yi tare da Sanata Sani Yariman Bakura.
Your browser doesn’t support HTML5