Shugaban kasa a zamanin mulkin soja, marigayi janar Murtala Ramat Mohammed ne ya ayyana Abuja a matsayin wurin da zai zama sabon babban birnin kasar a shekara ta 1976, amma ba a tabbatar da Abuja a wannan matsayin ba sai a ranar 12 ga watan Disamba na shekara ta 1991, lokacin da wurin ya zama babban birnin tarayyar Najeriya. Wanda kafin wannan lokaci birnin Lagos ne aka sani da wannan matsayi.
A kidayar da aka yi a shekara ta 2006 an ce birnin na da mutane 776,298 wanda ya zo na takwas a cikin ayarin manyan birane a fadin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Abuja na daga cikin birane da ke habbaka cikin sauri a duniya. A shekara ta 2015 birnin Abuja ya karu da kashi 35 cikin dari na yawan al'umma, wanda ya sa aka yi kiyasin mutanen sun kai miliyan 6 a shekara ta 2016, wani abu da ya sa birnin ya zo na biyu mai yawan mutane bayan birnin lagos.
Abuja ba Jiha ba ce, saboda haka ba ta da hurumin yin zaben gwamna sai zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu.
Gwamnatin tarayya ta na nada ministoci biyu masu kula da birnin, daya babba, dayan kuma karamin minista. A yanzu akwai Minista Mohammed Musa Bello da mataimakiyarsa, kuma karamar Minista Rahmatu Tijjani. Minista Mohammed Bello shi ne na 16 cikin ayarin wadanda suka rike Birnin tun daga 1976.
Wannan Birni yana da kananan hukumomi 6. Ana zaben shugabanin kananan hukumomin a duk shekaru 3.
Shugaban hukumar zabe ta birnin tarayya, wato Resident Electoral Commissioner a turance. Alhaji Yahaya Bello, ya yi bayani cewa Abuja a shirye ta ke saboda duk abin da ake bukata na yin zabe an yi tanadin sa. Sai abubuwa uku ne ba a bada su ba, sune takardar kada kuri'a, sai takardar rubuta sakamako, na uku shi ne ma'aikatan wucin gadi.
Akwai 'yan asalin birnin tarayya wadanda aka same su a cikin Birnin Abuja da kewaye, yawancin su yan kabilar Gbagyi ne tun fil'azal. Suna da shugaban kungiyar yan asalin birnin Abuja da aka fi sani da OIDA, Pastor Danladi Jeji, ya yi bayanin yadda suka dauki zabe da ake yi a birnin musamman ma na shugaban kasa da na yan majalisun dokoki da kuma yadda ya shafe su.
Danladi ya ce akwai rudami a zaman su cikin Abuja, domin ya na ganin kamar sun rabu kashi biyu, ko Abuja ko Birnin tarayya, saboda haka suna rokon a tausaya a mayar da birnin ya zama jiha ta talatin da bakwai a kasar.
Malama Zainab Aminu, jami'a ce a hukumar zabe ta Najeriya, ta ce nauyin yin zaben kananan hukumomi 6 ya rataya a wuyan Abuja, ta kara da cewa birinin ya gudanar da zabukan kananan hukumomi shida a shekara ta 2022, saboda haka sai nan da shekara 2023 za a sake yin zaben, tunda akan yi shi ne bayan shekaru uku.
Ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris ne ake sa ran za a yi zaben shugaban kasa da na yan Majalisar Dokoki a babban birnin tarrayyar Najeriya.
Saurari cikakken rahotan Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5