Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ba da umurnin a nuna sakamakon kai tsaye ta allon lantarki.
Jami'in kawo sakamakon Farfesa Olabisi ya ce kananan hukumomi 16 ne a jihar Ekiti, ya kuma karanta sakamakon inda ya ce jam'iyyar APC ta Bola Tinubu ta samu kuri'u 201,404, yayin da PDP ta Atiku Abubakar ke bin baya da kuri'u 89,554. Ita kuma jam'iyyar Labour ta Peter Obi ta zama ta uku da kuri'a 11,397, yayin da jam'iyyar NNPP ta Rabi'u Musa Kwankwaso ta zo ta hudu da kuri'u 200 da 'yan kai.
Shugaban hukumar zaben Mahmood Yakubu ya ce an yi tsarin da za a samar da sufuri da ya hada da jiragen sama don jami'an kawo sakamako su iso Abuja daga dukkan jihohi don bayyana sakamakon.
Kwamishina a hukumar zaben Muhammad Haruna, ya ce ba wata matsala ta zahiri da za ta kawo tsaiko wajen gabatar da sakamakon wanda aka fara da jihar Ekiti, ya kara da cewa gaba dayan wadanda suka yi rijistar zabe a jihar Ekiti ba su kai miliyan daya ba, shi ya sa kusan a duk shekara suke fara gabatar da sakamakonsu.
Shugaban hukumar zaben Farfesa Yakubu ya daga gabatar da sakamakon zuwa karfe 11 na safiyar Litinin agogon Najeriya.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5