Zaben 2020: 'Yan Democrat Sun Gwabza Muhawara a Dare Na Biyu

Masu neman tsayawa 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Democrats sun gwabza muhawara a dare na biyu, inda aka tabo muhimman batutuwa irin su kiwon lafiya da shigowar bakin haure da kuma aikata manyan laifuka.

An yi matukar bugawa da daren jiya Labara, tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden, da sauran masu neman tsayawa takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Dimokarat, a kan batutuwan kiwon lafiya, da shigowar baki da matsalar aikata manyan laifuka, da kuma batun banbancin jinsi, a yayin da masu kalubalantar shi Biden din ke kokarin tunkude shi daga matsayinsa na dan jam’iyyar Dimokarat da ke kan gaba, wajen shirin karawa da Shugaba Donald Trump a zaben 2020.

“Ina takarar zama Shugaban kasa ne don in ceto ran wannan kasar,” irin shelar da Biden ya yi kenan a dare na biyu na muhawarar masu neman tsayawa takara a jam’iyyar Dimokarat, a kan wani munbari a birnin nan mai cike da masana’antu na Detroit a jahar Michigan.

Da Biden ya ce a ganinsa tsarin kiwon lafiyar da ‘yar takara Sanata kamala Harris mai wakiltar California ta yi tayinsa a wannan satin na cike da rudu, sai Harris, wacce ke tsaye ganga da Biden, ta mai da martani da cewa, “watakila dai ya rude ne saboda bai karanta ba.”

Biden ya yi watsi da wasu tsare-tsaren kiwon lafiya na gwamnati da Harris da sauran fitattun masu kalubalantarsa a jam’iyyar Dimokarat ke tayi, a maimakon haka, so ya ke a inganta tsarin kiwon lafiya na Obamacare, wanda aka bullo da shi yayin da ya ke Mataimakin Shugaban kasa Barack Obama.