ZABEN 2015: Matan PDP Sun Yi Gangami a Minna Jihar Neja

Hajiya Amina Namadi Sambo, matar Mataimakin Shugaban Nigeria.

Uwargidan Matamakin shugaban Najeriya ta jagoranci taron gangamin da matan PDP suka yi a Minna fadar gwamnatin Neja.

Hajiya Amina Sambo itace ta fara taron da sheilar jam'iyyar PDP.

Wadanda suka yi jawabai a wurin gangamin sun ce suna da karfin gwiwar jam'iyyarsu zata ci nasara a zaben mai zuwa. Suna ganin shugaba Jonathan shi zai cigaba da zama shugaban kasa.

Amina Sambo matar Namadi Sambo mataimakin shugaban kasa ita ta wakilci matar shugaban kasa Patience Jonathan. A cikin jawabinta Amina Sambo ta jawo hankalin mata da su cigaba da yiwa 'ya'yansu nasiha da addu'a. Su tabbata kada su bari 'ya'yansu su zama masu tada hankali. Tace a lokacin zabe da bayan zabe suna fata 'ya'yansu zasu zama masu bin doka.

Mai masaukin baki gwamnan jihar Dr Muazu Babangida Aliyu ya bayyana mahimmancin mata a faggen siyasa. Yace ba zasu yadda da wadanda basu san abun da suke yi ba sai rarumar kasa. Ba zasu yadda a mayar masu da Najeriya ta zama abun mutum guda ba kamar yadda ya faru a Legas. Jam'iyyar PDP ita ce ta kowa da kowa. Yace duk wanda yake jin idan ba dashi ba ba za'a yi komi ba to ya fita ya ga yadda zasu cigaba. Yace da yawa sun fita sun dauka zata rushe amma sai gata garam.

Amma shugabar matan APC reshen jihar Neja Hajiya Fatima Mustapha tace taron matan PDP din bai razanasu ba. Tace komi nasu sun barwa Allah.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Matan PDP Sun Yi Gangami a Minna Jihar Neja - 2' 44"