Rashin samun katunan zabe na din-din-din da karancin malaman zabe da kayan aiki sun kawo cikas wa 'yan gudun hijira dake jihar Borno duk da karin kwana daya da hukumar zabe tayi.
Wasu 'yan gudun hijiran sun koka da rashin samun katunan zabe da kuma rashin isowar jami'an zabe a lokacin da suke jiransu. Wadanda basu da katunan zabe ba'a bari sun kada kuri'a ba.
Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi kwamishanan zabe na jihar Borno akan koken 'yan gudun hijiran. Yace wasu sun bugo masa cewa malaman zabe basu isa sansanonin ba. Yace lamarin ya damesu domin sun riga sun sanar cewa sun raba kayan aiki kuma malaman sun tafi wurin zaben. Yace abun da ya jawo jinkirin shi ne wasu sun ki su bada motocinsu domin su kai jami'an zabe sansanonin. Wasu kuma sun ji tsoron tafiya da dare saboda yanayin tsaro.
Yanzu dai ana jiran sakamakon zabe ne.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5