ZABEN 2015: Jang Ya Kira INEC Ta Gudanar da Zabe Mai Adalci

Gwamnan jihar Filato Jonah Jang

Gwamnan jihar Filato ya kira hukumar zabe ko INEC tayi tsayin daka ta gudanar da zabe mai adalci.

Gwamnan yayi kiran ne lokacin da ya karbi nashi katin zaben ko PVC.

Da yake magana akan shugaban hukumar zabe Farfasa Jega, gwamna Jang yace mutum ne mai tsare gaskiya. Idan ya tashi yin abu yana yi ne da gaskiya. Sabili da haka sun sanshi. Gwamna Jang yace dalili ke nan da ya fada masa cewa a wannan karon kada ya bari sunan da ya gina ya lalace. Yace idan sunan ya lalace su da suka sanshi ba zasu ji dadi ba.

Jonah Jang yace Allah ne mai ba mutum shugabanci sabili da haka duk wanda ya ba shi ke nan. Dangane da wadanda ke shirin tada hankali yace jami'an tsaro sun shirya zasu kuma hadu da irin wadannan mutanen.Yace Najeriya ta gaji da jinin da ake zubarwa.

To saidai an samu wasu matsaloli kamar yadda wasu katunan zaben da aka raba sun fito babu suna babu hoto. Akwai wasu kuma sun samu katuna fiye da guda daya.

Kwamishanan zaben jihar Filato Dr Godwin Kwanga yace batun katunan da babu sunaye a kansu kamar yadda mutum ke sake kwafar wani abu a naura wani zibin sai takardar ta fito babu komi hakan ya faru da wasu katunan

To saidai wadanda basu samu katinsu ba kwamishanan yace akwai wasu katuna dake tafe tana yiyuwa nasu na ciki. Kwamishanan ya kara da cewa bayan da suka yiwa mutane rajista a watan Nuwamban bara sun gano cewa wasu mutane 35,000 suka yi rajista fiye da sau guda. Sabili da haka ire-iren wadannan mutanen zasu samu matsala.

Dangane da wadanda suka samu katuna fiye da guda kwamishanan yace watakila mishkila aka samu wajen buga katin.Amma zasu baiwa mai katin guda daya kacal.

Ministar Albarkatun Ruwa Mrs. Sarah Ochekpe ta yabawa hukumar zaben kan yadda take gudanar da aikinta da yin tsokaci akan wadanda suka yi rajista fiye da sau daya.

Ga rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN2015: Jang Ya Kira INEC Ta Gudanar da Zabe Mai Adalci - 3' 26"