ZABEN 2015: Jam'iyyar MPP Ta Shigarda Kara a Kano

INEC

Jam'iyyar Mega Progressive Party ko MPP ta shigar da kara a kotun sauraren korefe-korafen zabe reshen Kano saboda cire sunanta daga jerin jam'iyyun da suka tsaya takara.

Wadanda jam'iyyar ta gurfanar a kotun zaben sun hada da Onarebul Barau Jibrin da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya dukanninsu 'ya'yan jam'iyyar APC su ne kuma wadanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wadanda suka lashe zaben kujerun sanata a mazabun Kano ta kudu da ta arewa.

Alhaji Isa Nuhu Dan Fulani shugaban jam'iyyar MPP ya bayyana dalilansu na tafiya kotu. Yace sun kai kara bisa ga ciresu daga jerin masu takarar kujerun sanatoci guda uku a jihar Kano. Suna rokon kotun ta biyasu hakinsu akan yadda hukumar zabe ta ki buga sunayen 'yan takaransu da kuma tambarin jam'iyyarsu.

Da suka ga babu sunan jam'yyarsu sun yi kokari su sanarda hukumar zabe domin tayi gyara amma da aka zo zaben babu sunansu. Yace sun kai hukumar zabe kara tare da duk wanda yake ikirarin ya ci zaben sanata a Kano. Suna bukatar hukumar ta rushe zaben a sake wani dasu idan basu ci ba to shi ke nan hankalinsu zai kwanta.

Banda karar da MPP ta shigar shi ma dan takarar jam'iyyar PDP Bashir Garba Lado daga mazabar Kano ta tsakiya ya shigar da nasa korafin gaban kotu inda yake kalubalantar nasarar Rabiu Musa Kwankwaso na APC gameda zabensa.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Jam'iyyar MPP Ta Shigar da Kara a Kano - 2' 12"