Matasan sun ce sun gaji da yadda 'yan siyasa ke anfani da addini da kabilanci wajen haddasa rikici tsakanin al'umma.
Shugaban matasan ya bayyana makasudin shirya taron. Jeremiah Mareng daya daga cikin shugabanin matasan yace suna neman canji amma da zaman lafiya domin irin wurare kamar su Maiduguri babu zaman lafiya. Ko a Filato an samu rashin zaman lafiya. Yace amma su matasan sun gane cewa wasu ne suke anfani dasu domin su cimma burinsu. Yace babu wanda ya kamata su goya ma baya sai Janar Buhari.
Wani Adamu Jeji yace yana tabbatarwa duniya cewa da ikon Allah APC ce zata kafa sabuwar gwamnati ta kuma kawo canji. Idan sun kafa gwamnati a Filato suna da abubuwan da zasu tanadawa matasa domin su daina tada hankali.
Mahalarta taron sun hada da matasan musulmi da na kirista daga unguwanni daban daban wadanda a da can basa ko ga maciji da juna. Wani yace da sun fuskanci matsaloli da dama amma yanzu kawunansu sun waye. Yanzu sun hada kai kuma ba zasu bari a kawo masu banbancin addini ko na bangaranci ba.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5