Zabe: Hukumar 'Yan Sandan Najeriya Ta Gargadi Masu Kalaman Batanci

Mukaddashin Shugaban Yan Sandan Najeriya, Muhammaed Adamu Abubakar

Yayin da zaben najeriya ya rage kwanaki uku, yanzu haka ana samu karin kalaman batanci daga bakin 'yan siyasa wanda ka iya tunzura magoya bayansu wajan aikata ba daidai ba, musamman a tsakanin jam'iyyun APC da PDP.

Yayin da ya rage saura kwanaki uku a gudanar da babban zaben Najeriya, mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya, Muhammed Adamu Abubakar, ya gargadi ‘yan siyasa da su guji tayar da rigingimu a lokacin zabe.

Abubakar ya kara da cewa hukumarsa za ta yi aiki ba sani ba sabo tare da tallafin sauran hukumomin tsaro wajan gano wani ko wasu gungun mutane da suke son ya yi wa dimokradiyya karan tsaye.

Kafin wadannan kalaman nasa, dukkan jam’iyyun Najeriya sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya, kafin lokaci da kuma bayan zabe, a karkashi kwamitin zaman lafiya da tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalam Abubakar ke jagoranta.

Yanzu haka dai manyan jam’iyyun kasar wato APC da PDP suna zargin junansu na shirin ta da hankali a lokacin wannan zabe, zargin da kowane bangare ya musunta.

A wani bangaren kuma, kungiyoyi fararen hula a karkashin cibiyar CITAD wadda take fitar da rahoto na wata-wata kan bicike da bibiyar kalaman batanci ta kafofin sada zumunci da sauran kafafan yada labarai, cibiyar ta ce ta lura da kyau cewa kalaman batanci masu nasaba da addini sun yi sauki a kafafan sada zumunta.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina da kuma rahoton Mahmud Ibrahim kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Zabe: Hukumar 'Yan Sandan Najeriya Ta Gargadi Masu Kalaman Batanci