Yanzu haka kwanaki biyu suka rage a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na jihohi a Najeriya, da alamu dai da sauran rina a kaba game da zaben gwamna a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Adamawa.
A karon farko uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi magana kan batun siyasar jihar Adamawa, tana mai cewa cancanta za’a yi a jihar ba zaben “SAK” ba.
Tun bayan da jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta sha kayen zaben shugaban kasa a jihar aka soma nuna yatsa da zargin juna a tsakanin kusoshin jam’iyyar ta APC.
Aisha Buhari ta godewa Al’umma tare da yaba musu bisa nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben da aka yi na ranar 23 ga watan Fabrairu, sannan ta ce dole ne jama’a su tantance wadanda za su zaba a wannan karon ba zaben “SAK” ba.
Amma a martanin da jam’iyyar APC ta mayar ta hannun sakataran tsare -tsaren jam’iyyar a jihar Adamawa, Ahmed Lawal, ta ce ba za su lamuncewa wadanda ke yi wa jam’iyyar zagon kasa ba.
A wani labarin kuma, hukumar zabe mai zaman kanta INEC da kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar Taraba, Barr. Ibrahim El-Sudi, duk sun bayyana cewa har yanzu Alhaji Sani Abubakar Danladi, shi ne dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar ta Taraba.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun tarayya da ke jihar Taraba ta yanke jiya Laraba, inda ta dakatar da Abubakar daga tsayawa takarar gwamna, bayan da aka zarge shi da ba da takardun bogi na yawan shekarunsa ga hukumar zabe ta INEC.
Saurari cikakken rahoton Ibrahin Abdulaziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5