ZABEN 2015: Wasu Sojojin Ruwa a Legas Suna Kwace Katunan Zabe

Sabon Hafsin sojojin ruwa, Rear Admiral Usman O. Jibrin.

Bayan kammala raba katunan zabe da hukumar zabe ta INEC tayi wasu sojojin ruwa suna kwacewa mutane katunan zabe karfi da yaji.

Sojojin suna zarewa mutane ido ne su kuma rabasu da katunan zabensu ba tare da wata hujja ba.

Mustapha Muhammad wani mai sana'ar achaba dan asalin jihar Borno yace yana kan babur dinsa a unguwar Marine Beach a Legas sai sojin ruwa ya tareshi. Ya sa ya ajiye babur din gefe daya bayan ya cire makullin. Yayi watsi dashi na kusan mintuna goma sai da ya yi masa magana. Daga bisani sojan ya tambayeshi ko yana da katin zabe. Yace kafin ma ya fitar da jakarsa ta aljihu sojan ya kwace. Da ya cire katin zaben sai yace Mustaphan ya biya nera dubu goma sha biyar kafin ya bashi katin. Idan bashi da kudin sai ya dauki babur dinsa ya tafi ba tare da katin ba. Hakan ko ya faru.

Shugaban matasan yankin Alhaji Musa Shaburi yace abun da sojojin suke yi abun bakin ciki ne. Yace basu san manufar karbewa mutane katunansu ba, domin tamkar hanasu 'yancinsu ne.Yace sun gagara sanin dalilin da ya sa sojojin suna yin hakan. Yace har yanzu ba'a basu dalili ba.

Da aka tuntubi rundunar sojojin wani mai matsakaicin matsayi yace zasu bincika domin abun da yaransu su keyi shugabanninsu basu da masaniya.

Ga rahoton Babangida Jirin.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Wasu Sojojin Ruwa a Legas Suna Kwace Katunan Zabe - 2' 38"