Za'a yankewa Charles Taylor hukunci

Wannan wani mutum ne mai suna Jabati Mambu, wanda yan tawaye karkashin jagorancin Charles Taylor suka yankewa hannun dama shekaru 13 da suka shige. Yana tsaye ne a harabar ginin Majalisar Dinkin Duniya a Freetown kasar Saliyo.

Alhamis idan Allah ya yarda kotun aikata laifuffukan yaki ta musamma zata yanke hukunci a shari'ar da aka yiwa tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor

Alhamis din nan idan Allah ya yarda, kotun shari'ar laifuffukan yaki, wadda Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya, zata yanke hukunci a shari'ar da aka yiwa tsohon shugaban Liberia Charles Taylor.

Wannan kotu ta musamman da aka kafa domi shari'ar laifuffukan yaki da aka aikata a kasar Saliyo ta caji Mr. Taylor da laifin aikata laifuffukan yaki guda goma sha daya da laifuffukan galazawa bani Adamu da kuma wasu laifuffukan da suka danganci keta ka'idodin dokar kasa da kasa a saboda zargin da ake yi masa na goyon bayan yan tawayen Saliyo a lokacin yakin basasar da aka yi a Saliyo.

Mr Taylor bai amsa laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa ba.

Anyi shari'ar shekaru hudu a Hague kasar Holland ko Netherlands domin tsoron cewa kila yi masa shari'ar a Saliyo zata hadasa tarzoma a yankin.

An dai zargin tsohon shugaban na Liberia da laifin baiwa kungiyar 'yan tawayen Revolutionary United Front makamai, domin ramar wa kura aniyarta kuma a bashi lu'u'lu'u da ake hakowa a gabashin kasar Saliyo.

Ana cajinsa da cewa shine keda alhakin yin kisa da yiwa mata fyade da ta'adanci da daukar yara aikin soja da kuma tilastawa jama'a yin bauta..

Kimamin mutane rabin miliyan ne aka kashe a yakin basasar Saliyo da aka shafe shekaru goma sha daya ana yi. A shekara ta dubu biyu da biyu aka kawo karshen yakin.

A shekara ta dubu biyu da shidda aka kama Charles Taylor. A yayinda shari'a kotu ta saurori jimilar bayani daga shedu dari da goma sha biyar na dukkan bangarorin.