Za Mu Yi Takarar ‘Yan Majalisu- Lumana

Wani dandazon jama'ar Jamhuriyar Nijar

Jam’iyyar adawa ta Lumana Afrika a Jamhuriyar Nijar ta musanta rade-radin da ake na cewa ba za ta tsayar da dan takara majalisa ba a jihar Maradi.

A ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu za a yi zaben shugaban kasa hade da na ‘yan majalisu a kasar ta Nijar.

Darektan yakin neman zabe jam’iyyar, Malan Tsalha Abdu a wata hirar da ya yi Muryar Amurka, ya ce wasu ne kawai suke so su janyo rudani a zaben.

“Yanzu haka duk hankalin mutane duk ya tashi, an ce Lumana ba ta yin takara gaba daya a jihar Maradi.” In ji Abdu.

Ya kara da cewa “abinda na ke kira ga masu goyon bayanmu su tafi su karbi katunsu na zabe, su tafi ranar zabe tun da sassafe su yi dafifi su yi zabe, su kasa su tsare kuma su raka.” In ji Darektan yakin neman zaben jam’iyyar ta Lumana.

Saurarin cikakkiyar hirar da Muryar Amurka ta yi da MalaN Tsalha Abdu:

Your browser doesn’t support HTML5

Za Mu Yi Takarar 'Yan Majalisu- Lumana- 2'02"