Yayinda har yanzu ba a tsayerda ranar zaben kananan hukumomi ba a jamhuriyar Nijer Kotun kolin kasar ta sanar cewa bisa tsarin doka wa’adin shuwagabanin kananan hukumomin da na kansilolin na kasar 265 da aka zaba a watan Fabrairun 2011 zai kammala a cikin wannan watan da muke ciki.
A sakamakon gardamar da ta barke tsakanin jamiyyar dake mulki da wadanda ke adawa a yayi wani taron majalisar tattauna al’amuran siyasa wato CNDP, ne shugaban wannan majalisa Firaminista, Birji Rafini, ya bukaci kotun Conseil d’etat, ta fayace matsayin doka akan wa’adin na kansiloli da shuwagabanin kananan hukumomi 265, ganin cewa har yanzu babu almar shirya zaben da zai bada damar maye guraben wadanda suka shafe shekaru biyar suna mulkin al’umomin karkara.
Yanzu dai Kotun tace bisa La’akari da cewa ba daya rana shuwagabanin suka fara aiki ba saboda haka wa’adin mulkinsu zai kamala daga ranar 17, zuwa 25, ga watan nan na Fabrairu.
Jami’yyar PNDS, Tarayyar mai mulki na ganin cewa akwai bukatar karawa Kansilolin da shuwagabaninsu wa’adi domin rikon kwarya har zuwa lokacin da za’a gudanar da zaben sabbin wakilai.
Sanarwar Kotun tazo ne a wani lokaci da bangarorin soiyasar ta Nijar, suka bukaci Gwamnatin kasar ta samar masu alfarmar hukumar zabe ta kasar CENI, domin ta dage zaben kananan hukumomi daga ranar 9, ga watan Mayun 2016, zuwa karshen shekara saboda dalilai na rashin shirya wanann zabe in ji su.