Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da ba da tallafin naira biliyan daya ga ‘yan kauswar da ibtila’in gobara ya shafa a jihar.
Da safiyar ranar Lahadi, kasuwar Monday Market wacce ke Maiduguri, babban birnin jihar ta kama da wuta.
Har yanzu hukumomin jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ba su fayyace musabbabin gobarar ba, wacce ta lakume shaguna da dama.
“Na ba da umurnin a saki naira biliya daya domin mu yi gaggawar tallafawa wadanda wannan gobara ta shafa, saboda mun san cewa wasu daga cikin su, za su iya fuskantar matsalolin rayuwa cikin ‘yan kwanakin da ke tafe. Da yawa daga cikin su, na dogaro da kasuwancin da suke yi a kullum domin samun biyan bukata.”
A cewar Zulum, zai kai kokensa zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin neman a tallafawa ‘yan kasuwar da lamarin ya shafa.
“Ina mai kira da kowa ya kwantar da hankalinsa. Na san abin da ku ke ji, za kuma mu tallafa muku ta kowace hanya da iznin Allah.” Zulum ya kara da cewa.