SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da iyalan jami'an tsaron da aka kashe fagen daga ke cewa suna fuskantar kuncin rayuwa.
Jami'an tsaron Najeriya sun jima suna shedawa jama'ar kasar cewa sun shirya tsaf ga kare rayuka da dukiyoyin jama'a, sai dai har yanzu matsalar a wasu wurare sai kara habaka take yi.
A Jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, yankin gabashin Jihar shi ne ya jima cikin matsalar kafin ta bazu zuwa wasu yankuna, kuma har yanzu batun bai sauya ba.
Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni kuma yanzu mai baiwa gwamnan Sokoto shawara na musamman Abdullahi Muhammad Tsamaye, ya ce har yanzu ‘yan bindiga na addabar jama'a, domin ko kwana biyu da suka gabata an kai hare-hare a wasu kauyuka inda aka kashe wasu mutane aka yi garkuwa da wasu, ya ce suna fatar jami'an tsaro za su kara azama ga maganin matsalar.
A nata bangaren, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce tana sane da matsalolin, shi ne ma ya sa yanzu take bitar yanayin tsaro don kara kimtsawar tunkurar lamarin.
Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Sakkwato Muhammad Usaini Gumel ya ce babban sufeton ‘yan sanda ya basu umurnin kara tabbatar da tsaro a yankunansu, kuma akan haka ne ya taro jami'an DPO da manyan jami'ai su tattauna yadda zasu kara samar da tsaron.
Shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista a Sokoto Rev. Fr. Nuhu Iliya, ya ce suna fatan jami'an za su kara azama ga samar da tsaron domin yanzu lokuta ne da wasu kan iya shiga ko ina saboda haka suna son jami'an kara yin kokari bisa ga wanda suke yi.
Haka kuma wannan na zuwa ne lokacin da iyalan jami'an ‘yan sanda da suka rasa rayukan su bakin aiki ke cewa rayuwa tana yi musu kunci saboda rashin masu kula da yi musu hidima.
Nafisa Muhammad daya ce daga cikin matan da aka bari da marayu ta ce mijinta ‘dan sanda ne an kashe shi bakin aikinsa tun shekarar 2018 amma har yanzu basu samu komi ba kuma rayuwa ta yi musu tsami ita da yaranta.
Akan lura da hakan ne ya sa kungiyar matan jami'an ‘yan sanda ta yanke shawarar tallafawa wasu daga cikin su ta hanyar koya musu sana'o'i don dogaro da kai da kuma basu tallafin abinci.
Shugaban kungiyar Aishatu Muhammad Gumel ta ce sun lura cewa matan ‘yan sanda ko yaushe suna fuskantar damuwa saboda rashin tabbas na rayukan mazansu dake fita aikin samar da tsaro, wasu ana barin su da marayu suna ta wahala shi ya sa suka nemi tallafi daga gwamnatin Sakkwato don taimakawa iyalan wadanda suka rasa mazansu.
Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da daukar rayukan jama'a , da tarwatsa garuruwa tare da kawo asarar dukiya mai yawa, duk da yake mahukunta na kan kokarin magance matsalar.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5