Za Mu Samu Nasara A Kotu - Gwamnatin Najeriya

Ibrahim Kabir Masari

Gwamnatin Najeriya ta bayyana kwarin guiwar samun nasara a kotun sauraron karar zabe da za ta yanke hukunci a Larabar nan kan karar kin amincewa da sakamakon da ya kawo Ahmed Bola Tinubu karagar mulki.

Baya ga sanarwa ta musamman daga kakakin shugaban Ajuri Ngelale na kwarin guiwar samun nasara, mai ba wa shugaban shawara na musamman kan siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce ba sa shakka ko kokonton samun nasara.

Yana mai cewa, “Aikin gama ya riga ya gama. Allan da ya ba da wannan nasara ga lokacin zabe shi zai kara tabbatar ma na da ita a lokacin shari’ar.”

Ita ma jam’iyyar APC ta bakin sakataren ta na labaru Felix Morka ta ce Tinubu ya lashe zaben na 25 ga watan Febereru don haka su na da kwarin guiwar kotun za ta tabbatarwa Tinubu nasarar sa.

A Tatihin shari’un da a ka yi a baya tun fara wannan dimokradiyya a 1999 ba a taba soke zaben shugaban kasa a nada wani ko a sake zaben ba.

In za a tuna a zaben 2007, alkalai 7 ne a kotun koli su ka yanke hukuncin karkashin marigayi Jostis Idris Legbo Kutigi inda aka samu canjaras na alkalai 3 su ka soke zaben marigayi Umaru ‘Yar’adua yayin da uku su ka ce zaben ya yi daidai. A nan dai Kutigi ya raba gardama da kuri’ar sa ya marawa masu cewa zaben ya yi daidai baya.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

INSERT OF IBRAHIM KABIR MASARI ON TRIBUNAL.mp3