Shugaban Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta gudanar da sahihin zabe wanda zai zamanto karbabbe ga dukkan ‘yan takara da masu kada kuri’a.
A cewar Buhari, zabukan da aka yi a baya-bayan nan, alamu ne da ke nuna cewa tsarin dimokradiyyar kasar na ci gaba da bunkasa.
“Tun daga 2015, yadda muke gudanar da zaben ya inganta babu kakkautawa, tun daga zaben 2019 zuwa zabukan da suka biyo baya a Edo, Ekiti, Anambra da jihar Osun, sun gudana ta yadda ‘yan takara da masu kada kuri’a suka nuna gamsuwarsu, hakan kuma muke fatan gani a zaben 2023 karkashin sa idon kasashen waje.”
Buhari, ya bayyana hakan ne a karshen makon nan, yayin jawabin da ya yi a taron da Cibiyar wanzar da zaman lafiya ta USIP ta shirya a gefen taron da shugabannin Afirka suka yi da Shugaba Joe Biden a Washington D.C.
Shugaban na Najeriya ya kuma tabo batun yadda gwamnatinsa take yaki da matsalar cin hanci da rasahawa.
A kididdigar da ta yi a 2021, Kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa, ta ce Najeriya ce kasa ta 154 a duniya, da ti fama da matsalar cin hanci da rashawa cikin kasashe 180.
Sai dai Buhari ya ce, matakan da suke dauka suna kai kasar ga gaci.
“Hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa na ci gaba da bankado kudade da samun nasara a kotu ta hanyar hukunta wadanda suke yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.”
Wata babbar matsala da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya ita ce ta tsaro, wacce ta yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da asarar dukiyoyi.
A arewa maso gabashin kasar, kasar na fama da mayakan Boko Haram da ISWAP, a arewa maso yammaci tana fama da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sai a kudancin da take fama da ‘yan awaren Biafra.
Amma Buhari ya ce jami’an tsaron kasar suna samun galaba, musamman akan mayakan Boko Haram.
“Ya ce idan za ku iya tunawa, a lokacin da na hau mulki, kungiyar Boko Haram na rike da kashi biyu cikin uku na jihar Borno, rabin jihar Yobe da wasu kananan hukumomin jihar Adamawa, amma yau, ba haka lamarin yake ba.”
Buhari ya kara da cewa, duk da wadannan nasarori, yake-yaken da ake yi a kasashen makwabta ko a yankin Sahel da ma yakin da ake yi a Ukraine, na yin mummunan tasiri akan Najeriya duba da yadda ake samun kwararar makamai daga wadannan yankuna.
Ya kara da cewa Najeriya da Amurka, na da kamanceceniya ta fuskoki da dama musamman kan abin da ya shafi yaki da ta’addanci da matsalar sauyin yanayi.
A shekarar 2015 da Shugaba Buhari ya karbi mulki, ya yi makamancin wannan jawabi a zauren cibiyar na USIP, inda a karshe aka ba mahalarta taron damar yi masa tambayoyi, sai dai a wannan karo an samu akasin haka - lamarin da ya sa wasu suka fusata.
“Dalili kenan da ya sa muka baro inda muke, muka zo wannan taro, amma ko tambaya daya ba a bari mun yi ba.” In ji daya daga cikin masu korafin da bai bayyana mana sunansa ba.
Bisa al’ada irin wannan taro bai rasa halartar masu zanga-zangar lumana da kan kafa dandali a kofar shiga zauren cibiyar ta USIP.
A wannan karo, wasu mutane dauke da kwalaye da aka yi rubutu daban-daban, kamar na neman a kubutar da dalibar nan Leah Sharibu wacce Kirista ce da mayakan ISWAP suka sace a jihar Yobe tun a 2018, da neman a bi ya wa Deborah kadinta, dalibar da ake zargi wasu dalibai sun kashe a jihar Sokoto bayan da aka zarge ta da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.
Taron ya samu halartar ‘yan Najeriya mazauna Amurka, kungiyoyi kare hakkin bil Adama, da masu rajin kare tsarin dimokradiyya da kuma ‘yan jarida.
Najeriya na shirye-shiryen gudanar da babban zabe a watan Fabrairun badi, inda za a zabi shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin tarayya, sai kuma a watan Maris da za a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5