Wasu na ganin an mayar da shugabanin Afirka kamar yara kanana, sai kiran su ake yi zuwa kasashen Turai, yayin da wasu kuma na ganin salon siyasar duniya ce ta sauya saboda haka kowa na kokarin zawarcin kasashen Afirka masu dimbin ma'adinai.
Shugaban Amurka Joe Biden da Shugabanin Afirka zasu fara wani taro a yau Talata.
Rahottani da ke fitowa daga Ofishin jakadancin Amurka na nuni da cewa wannan taro da Shugaban Amurka Joe Biden ya kira zai nuna muhimmancin dangantakar Amurka da Afirka da kara yin hadin gwiwa kan muhimman batutuwa da suka shafi duniya baki daya, kama daga harkar tsaro da ta'addanci da batun canjin yanayi, sannan da cin hanci da rashawa, saboda ana ganin Nahiyar Afirka za ta tsara makomar duniya nan gaba ba kawai makomar mutanen Afirka ba.
Amma ga masanin harkokin siyasa da gudanar da mulki kuma malami a jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk, yana ganin akwai abin dubawa a yadda kasashen Turai ke gaiyatan shugabanin nan Afirka.
Farouk ya ce sun zama kama yara wadanda manya kasashe ke kira domin a gaya masu abinda za su yi, ba su da martaba a gaban wadannan manyan kasashen duniya.
Shi ma kwararre a harkokin kasuwanci da dangantaka na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya ce wannan irin taro abu ne da ke nuni cewa ana zawarcin Nahiyar ne saboda irin arzikin da Allah ya yi mata.
Mikati ya ce Nahiyar Afirka na da mutane sama da biliyan daya, kuma akwai matasa masu yawa a Nahiyar. Daga ma'adinai irin su iskan gas, da zinari da wuraren noma, har wadanda ba sai an yi amfani da takin zamani ba. Mikati ya ce wannan arziki ne kasahen turan ke bukata shi yasa su ke kusantan Nahiyar.
Amma ga masanin harkokin diflomasiya da siyasar kasa da kasa kuma jami'in horad da 'yan majalisan Afirka da ke Abuja, Farfesa Usman Mohammed, ya ce duk ba a nan gizo ke saka ba. Shugabanin su gaya wa Amurka cewa lokaci yayi da za ta daina hada fadace fadace a tsakanin kasashe.
Usman ya ce shugaban Kasar Senegal Macky Sal shi ne kadai ya iya zuwa Rasha ya yi magana akan yadda Nahiyar Afirka ke wahala a sakamakon yakin Ukrain. Usman ya ce shugabanin Afirka sun riga sun zubar da darajar su domin cikunan su cike yake da bashi, ga kuma zalunci. Usman ya ce babu wani a cikin su da zai iya magana akan 'yanci.
A sakon sa na maraba, Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana fatan yin aiki tare da gwamnatocin Afirka, kungiyoyin jama'a, al'ummomi da kamfanoni masu zaman kansu don cigaba da karfafa ra'ayi game da makomar dangantakar Amurka da Afirka.
Saurari rahoton a sauti: