Za Mu Dakatar Da Kara Kudaden Haraji Kan Kayayyakin China - Trump

Shugaba Trump (Hagu) a gefen taron G20 da shugaba Xi Jingping na China (Dama)

Sai dai kasar ta China ba ta samu wani sassauci daga takunkumin da Amurka ta saka mata a baya.

Bayan wata ganawa da suka yi da takwaran aikinsa na China, Xi Jingping, Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai dakatar da shirinsa na sake kara kudaden haraji akan kayayyakin China da ake shiga da su Amurka.

Yayin da yake magana kan batutuwa da dama a wani taron manema labarai a karshen taron G20 na kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a Japan, shugaba Trump ya kume ce zai bar kamfanonin Amurka su rika sayar da kayayyakinsu ga babban kamfanin sadarawa nan na Huawei.

A baya Amurka ta haramtawa kamfanonin kasarta sayar da kayayyaki ga Huawei, bayan da jami’an tattara bayanan sirrin Amurka suka yi gargadi kan wata manhajar ta Huawei da ka iya zama barazana ga tsaron Amurka.

Sai dai kasar ta China ba ta samu wani sassauci daga takunkumin da Amurka ta saka mata a baya.

“Akalla a halin da ake ciki a yanzu, ba za mu dage takunkumin ba.” Inji shugaba Trump.