Za a Yi Wa Stevie Wonder Dashen Koda

Mawaki Stevie Wonder

Wannan sanarwa da Wonder ya yi, na zuwa ne yayin da a ‘yan kwanakin nan ake ta raderadin cewa ana yi masa aikin tsaftace jini da ake kira dialysis a turance, ko da yake babu wani rahoto da ya tabbatar da hakan.

Za a yi wa shahararren mawakin nan na Amurka Stevie Wonder dashen koda a watan Satumba mai zuwa.

Dan shekaru 69 da haihuwa, Wonder wanda ya taba lashe kyautar Grammy Award har sau 25, ya sanar da hakan ne bayan da ya kammala wani wasan mawaka a birnin London.

Mawakin ya ce tuni ya samu wanda ya ba da gudunmuwar kodar da za a dasa masa.

Ya kuma ce zai yi wasannin uku a nan gaba, kafin ya dauki hutu, amma ya tabbatarwa dumbin mutanen da suka halarci wasan mawakan cewa “yana cikin koshin lafiya.”