Za’a tuhumi Baturen nan da ayyana kanshi a matsayin mai akidar kyamar wasu jinsuna na Bil Adama, da laifin kisan mutane 50. Ana zargin mutumin da yiwa wasu masallata kisan gilla a kasar New Zealand.
Haka kuma 'Yan sandan sun ce mutumin dan asalin kasar Australiya, wato Brenton Harris Tarrant, dan shekaru 28 da haihuwa, har ila yau za’a tuhumce shi da laifuka 39 na kokarin kisan kai, inda zai bayyana a kotu karo na biyu a gobe Jumma'a, a babbar kotun dake birnin Christchurch a New Zealand.
Tarrant dai zai bayyana ta hanyar bidiyo ne daga kurkuku mafi tsaro a Auckland. Ba za’a nemi ya amsa ko ya musanta zargin da ake yi mashi ba a lokacin da zai yi bayyanin sa na biyu a kotu gobe jumma'a.
A can baya, an tuhumi Tarrant ne da laifin kisan kai guda daya lokacin da aka kama shi saboda hare-haren ta'addanci da ya kai ranar 15 ga watan Maris a kan masallatan al-Noor da Linwood ta amfani da makamai masu sarrafa kansu.