Za A Tasa Ƙeyar Diezani Zuwa Najeriya Domin Ta Fuskanci Shari'a

Tsohuwar ministar albarkatun man-fetur Diezani Aliason Madueke

Hukumar Ƴaki da Cin-Hanci da Rashawa ta EFCC ta samu damar tasa ƙeyar tsohuwar Ministar Albarkatun Man-Fetur Diezani Aliason Madueke zuwa gida Najeriya domin a gurfanar da ita a gaban kotu bisa zarginta da ake yi na halasta kuɗaɗen haram, a lokacin da take minista.

A sanarwar mai sa hannun Muƙaddashin shugaban sadarwa da hulɗa da jama'a na hukumar Yaƙi da Cin Hanci Da Rashawa da Ta'annati (EFCC), Dele Oyewale yace, sun samu izin kamawa da kuma tasa keyar tsohuwar Ministar Albarkatun Man-Fetur DIEZANI ALIASON MADUEKE zuwa gida Najeriya domin a gurfanar da ita bisa zargin da ake yi ma ta na Cin-Hanci Da Rashawa.

Ita dai tsohuwar Ministar ta albarkatun man-fetur ta fuskanci tuhumar karbar rashawa lokacin tana Ministar albarkatun man-fetur wajen bai wa wasu kamfanoni kwangila, kamar yadda hukumar binciken manyan laifuka ta ƙasar Ingila (NCA) ta zarge ta da shi, wanda hakan ya sa aka gurfanar da ita a gaban wata Kotu dake WestMinster a Ƙasar Ingila, sai dai kotun ta bada belinta akan fam dubu 70.

Oyewale, ya ce "gurfanar da tsohuwar ministar da akayi a wata kotu dake ƙasar Ingila abin a yaba ne, duk da cewa laifukan da suke zarginta da shi yasha bam-bam, sai dai ya ce "duk laifi, laifi ne, kuma babu wanda zai tsira idan har ya aikata laifi".

Oyewale, ya ƙara da cewa "hukumar EFCC na tuhumar DIEZANI ALIASON MADUEKE ne da laifuka 13, da suka haɗa da halasta kuɗaɗen Haram, kuma yanzu sun samu izinin kama ta da kuma tasa ƙeyarta zuwa gida Najeriya domin ta fuskanci Shari'ar laifuffukan da ake zargin ta aikata a lokacin ta na Minista".

Nasir Shu'aibu Marmara, masani ne kan lamuran da suka shafi tattalin arziki da zamantakewar yau da kullum, ya ce irin wannan tuhume-tuhume da kuma tasa ƙeyar masu laifi zuwa gida Najeriya ba sabon abu bane, domin sun sha faruwa, ƙarshe a yafe wa masu irin wannan laifuka.

Faruk Bibi Faruk manazarci ne kan tattalin arziki dake Jami'ar Abuja, ya ce wannan yunƙuri na EFCC wajen kamo da kuma tasa ƙeyar Diezani zuwa Najeriya, ba abin a yaba ba ne, ganin cewa tsohuwar Ministar ta shafe sama da shekaru 8 ba tare da wata huɓɓasa da hukumar ta yi na gurfanar da ita a gaban kotu ba.

Idan za a iya tunawa, a baya an tasa ƙeyar tsoffin gwamnoni irinsu James Ibori da Depreye Alamieyeseigha zuwa Najeriya domin su fuskanci Shari'ar cin-hanci da rashawa, ƙarshe kuma Gwamnatin Jonathan ta yafe musu.

Saurari rahoton Ruƙayya Basha:

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Tisar Ƙeyar Tsohuwar Ministar Zuwa Najeriya Domin Ta Fuskanci Shari'a