Yan majalisar sun sanar jiya Alhamis cewa, sun cimma yarjejeniyar da zata shata makomar sama da mutane dubu dari takkwas dake cin moriyar shirin da ake kira DACA, wanda ya shafi wadanda iyayensu bakin haure, suka shigo da su Amurka suna kanana, da kuma wadansu muhimman batutuwa a yunkurin yiwa shirin shige da fice garambawul da shugaba Donald Trump ya tsara.
Sai dai samun goyon baya ba zai zama da sauki ba. Banbancin ra’ayin jam’iyun kan batun yin garambawul a tsarin shige da fice, da kuma kasancewa ya rage kwana hudu kudin gudanar da aikin ya kare, ya sa kalubalar dake tattare da kafa dokar ta kasance da matukar girma.
Tun farko jiya alhamis, bayan jin labarin cewa, ‘yan majalisar dattijan suna dab da cimma matsaya, mai Magana da yawun fadar White House, Sarah Huckabee Sanders tace ba a riga aka cimma yarjejeniya ba tukuna, sai dai shugaba Trump yana da kwarin guiwar hakan.