Kasashe 16 da suka tsallaka zuwa zagayen kwaf daya a gasar cin kofin duniya ta mata na shirye-shiryen fara fafatawa.
A ranar Asabar za a bude zagayen da karawa tsakanin Switzerland da Spain, sai karawa ta biyu tsakanin Japan da Norway.
It dai Switzerland ta taka rawar gani a zagayen farko yayin da Spain ke kokari farfado da tagomashinta – musamman idan aka duba mummunan kaye da ta sha a hannun Japan.
It dai Japan ta lashe dukkan wasanninta uku a zagayen farko, inda ta kare a matsayi na daya rukuninsu.
Norway a nata bangaren tana cikin yanayi na rashin tabbas kan ko ‘yar wasanta Ada Hegerberg za ta samu buga wasan.
A ranar Lahadi Amurka za ta kara da Sweden yayin da a ranar Litinin Najeriya za ta fafata da Ingila.