Ana Neman Sanyawa Kaddarorin Yariman Saudiyya Takunkumi

Akwai kwararan hujjoji da suka alakanta yariman masarautar Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman da kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a watan Oktobar da ya gabata a ofishin jakadancin Saudi Arabia dake birnin Istanbul na kasar Turkiyya, a cewar wata jami’a mai bincike akan hakkokin jama’a a Malajisar Dinkin Duniya.

Agnes Callamard, mai bada rahoto ta musamman a Majalisar Dinkin Duniya akan kashe-kashen gilla, ta fada a wani sabon rahoto mai shafi 101 bayan da aka kwashe watannin 6 ana bincike, cewa kisan Khashoggi shiryayyen abu ne, kisan da aka yi ba bisa ka’ida ba wanda kuma kasar Saudiyya ke da alhakin sa a karkashin dokokin kasa-da-kasa.

Ta kuma ce za a sanya takunkumi akan kaddarorin yariman dake kasashen ketare har sai kuma an kara samun hujjojin da suka tabbatar da cewa bai da hannu a wannan kisan.

Ms. Callamard ta yi kira ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres akan ya fara bincike a hukumance akan kisan Khashoggi dan shekaru 59 da haihuwa, wanda don radin kansa yayi gudun hijira zuwa Amurka.