Za a Magance Labarun Karya A Nahiyar Afrika

Wasu kafafun sada zumunta

Yanzu haka dai Afirka na neman zama dandalin yada labaran karya ko "fake news" kamar yadda ake kira da Turanci. Wadannan labaru sun dade suvna jan hankali game da alaka tsakanin kafafen yada labarai da kuma aikace-aikacen siyasa a kasashe da suka ci gaba a baya-bayannan.

Wani bincke da aka yi ya nunawa cewa sama da rubu'i ko kashi daya cikin hudu (1/4) na ‘yan Najeriya da kasar Kenya da aka yi binciken a kansu, sun ce sun yada labarun karya da gangan.

Yanzu haka ma dai damuwar da ke cikin yada labaran karya ta yi sanadiyyar jefa kokwanto a zukatan ‘yan jarida game da ayyukansu na yada labarai, inda al’amura masu sarkakiya su ka shafi rayuwar al’umma kai tsaye.

To sai dai kuma tuni wasu kwararrun ‘yan jarida su ka yunkuro ta hanyar kafa shafin bindiddigi, domin yaki da wannan matsalar. Ibrahim Shehu Adamu wani tsohon ma’aikacin BBC ne da ke cikin wannan tawagar ta bindiddigi, ya shaida min manufarsu ayanzu.

Ya ce zuwa yanzu an fi nazartar wannan lamarin ne a kasashen Turai da kuma Amurka, amma idan aka kwatanta da halin-ko-in-kula da ake nunawa ga nahiyar Afrika, duk da cewa irin wadannan labarai na haddasa rasa rayuka ta hanyar yada zantuttukan kiyayya da wariyar launin fata, wanda mafi yawa ta hanyar shafukan sadarwa kamar Whatsapp, Facebook, da Twitter a nahiyar Afrika.

Ga Ibrahim Abdul-Aziz da cikakken rahoton

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Magance Labarun Karya A Nahiyar Afrika