Za’a fara ajiye gawar McCain a jihar Arizona, inda za’a yi wani zaman makokin da aka takaita mahalarta ranar Laraba mai zuwa, wanda kuma zai kasance dai dai da ranar cikar sa shekaru 82 da haifuwa. Al'ummar jihar zasu iya zuwa su yi mashi rakiya ta karshe a majalisar dokokin jihar.
McCain zai kasance sanata na 13 da za’a ajiye gawarsa a zauren majalisar dokokin kasa da ake kira Rotunda, karamci da aka kebewa fitattun 'yana kasa‘’ a cewar wanda ya zana ginin majalisar dokokin.
Za’a kuma gudanar da taro a Washington, wanda za’a yi a Cocin kasa da ake kira Washington National Cathedral ran Asabar mai zuwa. Ana sa ran cewa tsofin shuwagabnin kasa Barack Obama da George W. Bush zasu yi jawabai a wurin jana'izar.
Daga nan kuma za’a bine McCain a Makabartar makarantar mayakan ruwan Amurka a yankin Annapolis dake jihar Maryland. Za a binne shi kusa da babban abokinsa lokacin da suke makarantar mai suna Admiral Chuck Larson.