Za A Kara Megawatt 150 Kan Babban Layin Lantarkin Najeriya Kan Nan Da Karshen Shekara-Adelabu

Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

Za a samu karin lantarkin ne sakamakon nasarar kammala kashin farko na shirin samar da lantarki na shugaban kasa (PPI).

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, yace Najeriya ta kama hanyar kara megawat 150 kan babban layin lantarkin kasar kan nan da karshen shekarar 2024.

Adelabu ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin ganawa da manema labaran fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na Najeriya Bola Tinubu a fadar ta Aso Villa dake Abuja.

Ministan Lantarki Adebayo Adelabu

A cewarsa, za a samu karin lantarkin ne sakamakon nasarar kammala kashin farko na shirin samar da lantarki na shugaban kasa (PPI).

“Mun yi amanar cewa kafin karshen shekarar da muke ciki, za a samu karin wutar lantarki mai karfin megawat 150 da zarar an kammala kashin farko na ilahirin shirin.”

Kalaman ministan na zuwa ne a dai dai lokacin da babban layin lantarkin Najeriyar ke rushewa a karo na 12 cikin wannan shekara, abin da ya jefa milyoyin gidaje cikin duhu.