Za’a Kamalla Binciken Badakalar Ayyukan Hukumar NDDC A Watan Yuli - Akpabio

Nigerian Minister of Niger Delta, Godswill Akpabio

Ministan ayyukan yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya ayyana karshen watan Yuli a matsayin wa’adin kamala binciken kwakwaf na badakalar da ta mamaye ayyukan hukumar raya yankin Neja Delta wato NDDC.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bada umarin a yi wannan bincike don gano gaskiya kan lamarin da ya ki ci ya ki cinyewa.

Minista Godswill Akpabio, ya bayyana hakan ne a yayin fara aikin tantancewa na binciken a zahiri da ya gudana a otel din Ibom Golf Resort da ke birnin Uyo fadar gwamnatin jihar inda ya ce aikin binciken na daga cikin ayyukan gyare-gyaren cikin gida na hukumar NDDC.

Haka kuma, ministan ya ce, an zabi masu binciken ayyukan kudi na zahiri 16 ne don fara gudanar da aikin gano da tantance ayyukan da aka gudanar a yankin Neja Delta inda ya yi watsi da jita-jitar cewa binciken kwa-kwaf da ake yi, ya fara kaucewa hanya.

Yankin Neja Delta mai arzikin mai

Ya kara da cewa, wasu marasa kishin kasa ne ke ikrarin cewa, ana amfani da aikin binciken ne a matsayin dabara don ci gaba da shugabancin rikon kwarya na hukumar NDDC.

Akpabio ya kuma ce, suna bin umarnin shugaba Muhammadu Buhari ne, ta hanyar duba ayyukan da aka gudanar tun bayan kafa hukumar.

Kazalika, Akpabio ya ce, shugaba Buhari ya kuduri anniyar cewa, ba zai bar yankin Neja Delta da hukumar NDDC yadda ya same su ba a lokacin da ya haye kan karagar mulki, kuma don tabbatar da kawo ci gaban ne shugaban ya fitar da kudi daga kasafin kudin fadarsa don gudanar da aikin.

A nasa bangare, babban sakatare a ma’aikatar harkokin Neja Delta, Dakta Babayo Ardo, ya ce fara aikin tantancewar aikin a zahiri, wani mataki ne da ke nuna ci gaba matuka a kokarin gyara hukumar NDDC don gudanar da ingantaccen aiki yana mai cewa, an kammala aikin binciken hedikwatar hukumar kuma an fara bangaren aiki na gaba.

Taron Gwamnonin Yankin Niger Delta kan Shirin Koyarwa NDDC E-LEARNING PROGRAMME

A cewar Dakta Babayo Ardo, tawagar hukumar za ta kai ziyara jihohin yankin Neja Delta 9 don rangadin duba sama da ayyuka dubu 12 da hukumar ta gano.

Shi ma shugaban rikon kwarya na hukumar NDDC, Mr. Efiong Akwa, ya jadada cewa, aikin binciken kwa-kwaf din aiki ne na gaske kuma da gangan aka gudanar da aikin don gano bakin zare kan ayyukan hukumar, wanda hakan ya sanya ya zama wajibi a duba wuraren aikin a jihohi tara na Neja Delta kuma ya ce an umarci kwamitin ya ziyarce duk inda ayyuka sama da dubu 12 din su ke.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Mayun shekarar 2020 ne hadakar kwamitin majalisar dattawa da wakilai na Najeriya, ya yanke shawarar bincikar mambobin kwamitin rikon kwarya na hukumar ta NDDC kan zargin karkatar da tsabar kudi na naira biliyan 40 a cikin watanni 3.

Daga bisani majalisun biyu sun kafa kwamitin wucin gadi daban-daban don bincika ma'amalar kuɗi na kwamitin na rikon kwarya na hukumar NDDC wato IMC.

Idan za a iya tunawa dai, hukumar NDDC ta yi watsi rahotannin da suka mamaye kafafen yadda labarai da ke cewa ke a cikin wata uku ta kashe kudadden, ta na mai ikirarin cewa, bayanai daga babban bankin Najeriya ya ce, kwamitocin rikon kwaryar hukumar NDDC biyu ne suka kashe naira bilyan 81 da rabi tsakanin watan Oktobar shekarar 2019 zuwa watan Mayun shekarar 2020.