Za A Iya Wa'azantar Da Al'umma Ta Hanyar Barkwanci Da Nishadantarwa

B-Soja

Buhari Usman Makama, wanda aka fi sani da B-Soja- mawaki kuma mai gabatar da barkwanci domin nishadantar da masu sha’awar kallon barkwanci, ya ce yana isar da sakonnin raha tare da kama sana’ar barkwanci, domin zama mai dogaro da kai da isar da sakonnin ta hanyar barkwanci, kana da wa’azantar da mutane.

Ya fara barkwanci bayan da ya lura da cewar, da zarar ya bude baki wajen yin magana sai ya ga mutane sun fara yi masa dariya, da hakan ne ya san ya samu sana’a ta bawa mutane dariya.

Ya kara da cewa yana da kyau matasa su lura da irin baiwar da Allah yayi masu, wajen fito da irin baiwar su a bayyanar jama’a da amfani da ita ta hanyar da ya kamata.

Ya ce abinda ke ci masa tuwo a kwarya, daga cikin al'umma bai wuce yadda mutane ke kin yi masu uzuri da zarar an nemi su yi wani aiki kuma samu akasi, mutane basa uzuri sai kawai su yanke hukuncin cewar suna da girman kai da nuni da cewar su ma sunyi kudi basa kula mutane sai wanda suka zaba.

B Soja, ya kara da cewa har yanzu al'ummar Bahaushe bata farga da wannan dabi’ar ta “Standup Comedy” wato filin barkwanci da ake tara jama’a a biya kudi domin a baiwa mutane nishadi da barkwanci ba. Daga karshe ya ce babban burinsa bai wuce a san shi a duniya wajen bada labaran barkwanci da nishadantar wa ba.