Za a Hukunta Masu Taka Dokar Kariya Daga COVID-19 a Filin Jiragen Sama

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta yi gargadi kana ta nuna takaicinta bisa rashin da’a da wasu masu fada a ji a gwamnatin suka yi wajan keta dokar dakile yaduwar cutar COVID-19 a filin tashi da saukar jiragen sama na kasar. Ta kuma ce za a hukunta duk wanda aka kama da laifi, a daidai lokacin da ake kokarin hana ‘yan wasu kasashe shigowa kasar da nufin rage yaduwar cutar da ke ci gaba da barazana ga rayuwar al’ umma.

Babban Sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya bayyana takaicin gwamnatin kasar bisa keta dokar da aka shimfida a filin tashi da saukar jiragen sama ta kasar don kare al’umma daga kamuwa da cutar COVID-19 da wasu manya a cikin gwamnati suka yi.

Hukumar filin tashi da saukar jiragen sama a Najeriya FAAN, ta bukaci duk wani babba a kasar da ya bi matakan kariya daga cutar COVID-19 ko a hana shi shiga tashar jiragen saman kasar, kamar yadda shugaban hukamar Kaftin Rabiu Yadudu ya shaida wa Muryar Amurka.

Gwamnati dai ta dauki alwashin hukunta duk wanda ya ketare dokar matakan kariya, sannan ana kan binciken tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, da Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, wadanda ake zargin su da ketare dokar matakan kariya da aka shimfida a filin tashi da saukar jiragen saman kasar, babu wanda ya fi karfin doka a cewar Ministan Muhalli Muhammad Mahmud Abubakar.

A bangare guda kuma gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za a hana ‘yan wasu kasashe shigowa Najeriya a wani mataki na takaita yaduwar cutar ta COVID-19 wadda ya zuwa wannan lokaci adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura dubu 36, an kuma sallami mutane sama da dubu 15 daga asibiti, sannan an rasa mutane 789.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.

Your browser doesn’t support HTML5

Za a Hukunta Masu Taka Dokar Kariya Daga COVID-19 a Filin Jiragen Saman