Jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya jiha ce ta al’ummar Yarbawa, kuma su ke da fada a ji a bangarorin gwamnatin jihar, wannan ne karon farko da wani gwamna a jihar ya bada sunan bahaushe dan asalin arewacin Najeriya, amma haifaffen jihar, a matsayin wanda zai zama kwamishinansa.
Haka kuma akwai kakakin jam'iyar APC a jihar, Mr. Joe Igbeke dan kabilar Igbo da aka zaba, koda yake wannan ba shine karon farko da aka ba wani dan kabilar Igbo wannan mukamin ba, domin ko a zamanin tsohon gwamna Fashola, wani dan kabilar Igbo ya rike mukamin Akanta Janar a jihar.
Akitec Kabiru Ahmed da aka bada sunansa yanzu, ya taba rike mukamai daban-daban a baya a karkashin gwamnatocin da suka shude, inda ya rike mukamin shugaban hukumar zayyane-zayyane, da kula da muhalli a lokacin gwamana Fashola, ya kuma rike mukamin sakataren hukumar kula da ruwan sha a karkashin tsohon gwamna Ambode.
'Yan Arewa a jihar, ba a barsu a baya ba wajen yabawa da wannan rabon mukamai. Suna fadin cewa hakan yayi daidai domin zai taimaka wajen hadin kan al'umma da kasa baki daya. A karamar hukumar Agege dake jihar Legas aka haifi Kabiru Ahmed, sannan ya iya magana da harsuna uku, wato yarbanci da turanci, da kuma hausa.
Yanzu dai a yayin da ake jinjinawa gwamna Sanwo Olu, wasu 'yan Arewacin Najeriya na ganin har yanzu suna bin al’ummar Yarbawa bashi na nadin mukamai, musanaman idan aka yi la’akari da yadda gwamnoni, da ministoci 'yan Arewa ke baiwa yarbawa mukamai a Arewacin kasar.
Ko a kwanan nan ma, gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa'i, ya baiwa wata 'yar asalin yankin Yarbawa, amma haifaffiyar jihar Kaduna mukamin kwamishiniya, banda masu bashi shawara da dama da yake dasu.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5