Matar dai wacce EFCC ta kama da ke jerin mutanen da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ke nema, ta yi amfani da hanyar musanya kudi ta yanar gizo.
Shugaban EFCC shiyyar Benin Mukhtar Bello yace an kama matar, waddda bai ambaci sunan ta ba, da take damfara ta hanyar musayar kudin BITCOIN, inda ta kan tara bayanai jagororin kamfanoni, ko kasuwanci masu hulda da ketare ta turawa 'yan uwan hadin bakin ta na Amurka, da ke aiwatar da damfarar.
Dama shugaban hukumar yaki da cin hancin Ibrahim Magu, ya bugi kirjin kama 'yan damfarar duk da sukar da hukumar ke sha na zabar wadanda ta kan yi wa dirar mikiya, da kyale wasu da ke danyen ganye, da gwamnati.
EFCC ta ce ta samu motocin alfarma a wajen matar kuma za ta gurfanar da ita a kotu a nan Najeriya bayan kammala dukkan bincike.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5