Shi dai wannan karamin ofishin jakadancin da ake kira consulate a Turance, ana gida shi ne a acre 12.2, a wani sabon fege na zamani da ke wani tsibiri da aka samar na kan ruwa da ake kira Eko Atlantic.
Wannan katafaren ofishin jakadancin da ake fatan zai zama mafi girma a duniya idan aka gama shi a shekara ta 2027, zai samar da aikin yi ga 'yan Najeriya 2500, akasarinsu injiniyoyi, Masu Zayyane zayyanen gidaje, ma aikatan ofis da kuma leburori.
A cewar jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, wannan gini na da mahinmancin gaske wajen kara dankon dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya dama nahiyar Africa.
Mr Stephen Ibelli, kakakin ofishin jakadancin Amurka a Legas, ya ce ba karamar dangantaka ce tsakanin Najeriya da Amurka ba. Na farko dai Najeriya babbar kasa ta demokiradiyya a Afurka, itace mafi girma, kuma tattalin arzikinta shi ne mafi girma a Afurka.
Akwai danganta tun shekaru fiye da 60, kuma yanzu haka akwai 'yan asalin Najeriya fiye da dubu 500 a Amurka, akwai yan Najeriya fye da dubu 100 da ke shiga da fita Amurka, akwai dalibai fiye da dubu 13 dake karatu a Amurka...
To ko yaya 'yan Najeriya ke kallon wannan kawance na Amurka da Najeriya? Dr Fati Sulaiman, wata wadda ta ci gajiyar wannan dangantaka ta Amurka da Najeriya ta fuskar ilimi, ta bayya hakan a hirarta da Sashin Hausa.
Ko gabanin zaben shekara ta 2015, Amurka ta shige gaba wajen ganin an samu amintaccen zabe a Najeriya, bayan taimako ta fuskar tsaro da take baiwa sojojon Najeriya a yakin da su ke yi da 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP.
Saurari cikakken rahoton Babangida Jibrin:
Your browser doesn’t support HTML5