Wani babban jami'in Amurka ya ce Rundunar sojin Ruwan Amurka ta shirya tsab, don amfani da wasu sassa na sansanoninta wajen gina wasu dirka-dirkan wuraren tsare masu laifi, saboda rika tsare dubban bakin hauren da aka kama yayin yinkurinsu na ketare kan iyakar Amurka, muddun Ma'aikatar Tabbatar da Tsaron Ciki Gida ta Amurka ta bukaci hakan.
Jami'in ya tabbatar da bayanin da ke nuna cewa Rundunar sojin ta Amurka, ta rubuta takarda ga Sakataren Rundunar Sojin Ruwa Richard Spencer, mai bayanin wasu wurare a lungunan jahohin California, da Arizona da kuma Alabama, a matsayin inda za a iya kafa tantunan garkame duk wani baligi bakon haure da aka kama.
Daftarin takardar na nuna cewa Rundunar sojin Amurkar na iya tsare bakin haure kimanin 47,000 a kowanne daga cikin sansanoninta na jahar California - daya a San Francisco, daya kuma a kudancin Californiar. Takardar ta kuma ce ana iya tsare bakin haure kimanin 25,000 a wani sansanin da ke kusa da Mobite, jahar Alabama, sannan kuma wani adadi na bakin hauren na iya zama a wani rukunin tantunan a Yuma, jahar Arizona.