Za a Gayyaci Kwararru Wajen Rufe Tasoshin Nukiliyar Koriya Ta Arewa

  • Ibrahim Garba

Trump da Un

A wani al'amari mai ban mamaki, Shugaban Koriya Ta Arewa ya mika kai ga Amurka, ya na mai tabbatar da cewa zai rufe tasoshin nukiliyar kasar kuma zai gayyaci kwarru da 'yan jaridan Amurka da Koriya Ta Kudu su shaidi rufewar.

Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un na shirin gayyatar kwararru da ‘yan jarida daga Koriya Ta Kudu da Amurka don su zama shaida a lokacin da Koriya Ta Arewa za ta rufe tasoshin gwaje-gwajen nukiliyarta a watan Mayu, abin da jami’an Kaoriya Ta Kudu su ka fada kenan a yau dinnan Lahadi.

Sakataren Yada Labaran Shugaban Koriya Ta Kudu Yoon Young-chan, ya kuma ruwaito Kim na cewa, “Duk da yake dama can Amurka ta tsani Koriya Ta Arewa, da zarar mun fara tattaunawa za ta gane cewa ni ba irin mutumin da zai yi amfani da makamin nukiliya ba ne akan Koriya Ta Kudu ko kuma Amurka a ketaren Pacific.”

Kim ya kuma yi alkawarin canza agogon Koriya Ta Arewa ta wajen kara shi da minti 30, ta yadda zai daidaita da na Koriya Ta Kudu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kwarin gwiwa kan ganawar da aka shirya zai yi da Kim, bayan tattaunawar da su ka yi da shi da Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in da Firaministan Japan Shinzo Abe.