Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar Litinin 12 ga watan Disemba a matsayin ranar da za’a fara karbar katin zabe.
abuja, nigeria —
Hukumar ta ce duk wadanda basu karbi katin zabensu ba zasu je ofishin hukumar zaben dake kananan hukumomi 774 daga ranar 12 ga watan Disemba zuwa ranar Lahadi 22 ga watan Janairu.
Cikin sanarwar da babban kwamishinan INEC Festus Okoye ya fitar ranar Juma’a ya ce daga Juma’a 6 zuwa Lahadi 12 ga watan Janairu 2023 za’a fara karbar katin PVC a mazabu 8,809.
Sanarwar ta kara da cewa za’a dinga karbar katin daga karfe tara na safe zuwa uku na yamma dukkan ranaku har da Asabar da Lahadi.
Hukumar ta INEC ta umarci kwamishinonin zabe da su shirya taron masu ruwa da tsaki a jihohi da kananan hukumomi, don bayyana musu irin hanyoyin da za’a bi wajen karbar katin zaben ba tare da wata matsala ba.