Yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da coronavirus ya zarce miliyan 13 a fadin duniya, Amurka ta ce ta na sa ran fara samar da riga-kafin cutar nan da karshen bazara.
WASHINGTON D.C. —
Duk da cewa gwamnatoci na ta kara kakaba tsauraran dokokin killacewa da ba da tazara a tsakanin jama’a domin dakile yaduwar cutar.
Kafar yada labaran tattalin arziki ta talabijin CNBC a kasar ta sanar cewa, wani babban jami’in gwamnatin shugaba Trump ya fadawa manema labarai cewa tuni aka fara sarrafa riga-kafin duk da yake ba su da tabbacin wane ne zai bada abinda ake bukata.
An bayana Jami’in na cewa tuni suna nan suna sayen injina, da samar da guri da kuma kayayyakin hada magungunan.
CNBC ta ce ana sa ran kamfanoni biyu da za su yi aikin samar da riga-kafin, Modema da Johnson & Johnson za su fara gwajin maganin akan bil adama a karshen watan nan.