Bayan makonni da aka kwashe ana sauraren shaidu cikin sirri, Majalisar Wakilan Amurka mai rinjayen ‘yan Democrat, ta kada kuri’ar amincewa da fara shirin tsige shugaba Trump a baina jama’a, kan zargin cewa ya yi yunkurin tursasawa Ukraine ta binciki abokanan hamayyarsa na siyasa.
Mambobin majalisar sun bi jam’iyyunsu ne wajen kada kuri'ar ta shirin tsige shugaban, inda mambobi 232 suka amince kana196 suka nuna adawa da shirin.
Dukkan ‘yan jam’iyyar Republican sun ki amincewa da shirin tsige shugaban sai dai wasu ‘yan Democrat biyu da suka sauya sheka sun mara musu baya.
Nan da nan bayan kada kuri’ar, Trump ya shiga shafinsa na Twitter, ya kwatanta shirin binciken tsige shin, a matsayin "bita da kullin siyasa mafi girma a tarihin Amurka."