Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu wata hujja da za ta sa wani kwamiti mai karfi a majalisar dokoki yayi bincike akan kudaden sa.
"
Babu wani dan siyasa da zai fuskanci haka. Wannan shi ake kira cin zarafin sugaba. “abin tur ne kuma hakan na wulakanta kasarmu
,martanin da Trump ya maida kenan jiya Laraba a lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi akan matakin da kwamitin binciken sirrin majalisar wakilai ya dauka na binciken kudaden sa.
Shugaba Trump na wannan bayanin ne don ya auna shugaban kwamitin Adam Schiff, dan jam'iyyar Democrat, wanda ke yawan sukar shugaban.
Sa’o’i kafin wannan bayanin na Trump, Mr Schiff ya bayyana cewa kwamitin, wanda ke hannun ‘yan jam’iyyar adawar Democrat biyo bayan zaben rabin wa’adin da aka yi a watan Nuwambar bara, zai fadada bincikensa akan yiwuwar katsalandan Rasha, zai kuma duba ko damuwar Trump akan kudaden sa da dukiyar sa na da nasaba da manufofin da yake fiddawa da kuma wasu matakan da ya ke dauka a matsayin shugaban kasa.