Za'a Fara Amfani Da Mataimakin Alkali A Wasan Firimiya Lig

Hukumar shirya wasannin firimiya lig na kasar Ingila, tace shirya tsaf domin fara amfani da mataimakin alkalin wasa na Bidiyo (VAR) a gasar firimiya lig na shekara mai zuwa.

Hukumar tace a yanzu zata aika da bukatarta a hukumace zuwa ga hukumar Kungiyoyin kwallon kafa na kasa da kasa, da kuma hukumar kwallon kafa na duniya (FIFA).

An yi amfani dana'urar ta (VAR) a gasar cin kofin duniya na 2018, haka kuma ana amfani da ita a gasar Serei A, na Italiya da kuma Bundesliga na kasar Jamus, bayan haka kuma an yin amfani da ita a wasu gasar Carabao Cup na kasar Ingila.

Ku Duba Wannan Ma Za'a Haramtama Kungiyar Chelsea Siyan Zaratan 'Yan-Wasa

A watan Afirilu da ta gabata kungiyoyin kwallon kafa na kasar Ingila suka jefa Kuri'ar rashin yadda da amfani da ita nau'rar.

FA tace zata dauki matakin wayar wa magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa yadda na'urar take amfani.

Wani tsohon alkalin wasa mai suna Mark Halsey, yace yin amfani da na'urar yana da amfani, kuma zai taimaka sosai duk da kasantuwar jama'a da dama suna kyamatarta.