Tsohon Shugaban Amurka George H.W Bush ya rasu a jihar texas, asalin jiharsa, ranar Juma’a da yamma yana da shekaru 94 da haihuwa bayan ya kwashe shekaru masu yawa yana fama da rashin lafiya.
WASHINGTON DC, —
Za a kai gawar tsohon Shugaban Amurka George H.W Bush a wani bangaren ginin majalisar dokokin kasar, yayin da Amurkawa ke karrama shugaban Amurka na 41.
Za a budewa masu fada a ji da sauran jama’a ginin majalisar da ake kira "Capitol Rotunda" domin yi mashi karramawar karshe da yammacin yau Litinin har zuwa safiyar Laraba.
Bush, da ya yi wa’adi daya akan mulki a Fadar White House daga shekarar 1989-1993.
Za a yi mashi taron makoki ranar Laraba a majami’ar kasa da ke birnin Washington sannan a binne shi ranar Alhamis a dakin ajiye litattafai da karatunsa da ke jihar Texas.
Fadar White House ta sanar da cewa Shubaga Donald Trump zai halarci taron.