Za a Bude Gasar Tennis Ta Australian Open a Watan Fabrairu

Novac Djokovic, hagu da Rafael Nadal, dawa

Novak Djokovic da Rafael Nadal na shirin fara karawa a kakar wasa ta 2021 a gasar ATP ta Australian Open.

Za a fara gasar ne a ranar 2 ga watan Fabrariru inda fitattun ‘yan wasan za su wakilci kasashensu na Serbia da Spain.

Shararren dan was ana uku jerin gwanayen wasan tennis Dominic Thiem da dan wasa na 4 Daniil Medvedev na kasar Rasha za su yi wasa daban-daban a ranar bude gasar a Melbourne Park, inda a nan ne za a karbi bakuncin wasan karshe na Grand Slam daga ranar 8-12 a watan Fabrairu.

Kasar Serbia wacce ita take rike da kofin gasar ta hanyar jagorancin Djokovic da ya lashe gasar sau 8, za ta fara karawa da Canada a filin was ana Rod Laver sannan za ta kara da Jamus matakin rukuni-rukuni.

Thiem na kasar Austria da ya sha kaye a hannun Djokovic a wasan karshe a gasra bara a Melbourne, zai fara wasansa ne a filin was ana John Cain inda zai kara da dan kasar Italiya.

Nadal wanda na daga cikin ‘yan wasan da suka kara a karshe-karshe a gasar ta ATP zai kara da dan kasar Australia yayin da Medvedev zai gwada kaiminsa da takwaransa na Argentina.