Yiwa Yara Fyade Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya

A duk rana ta Allah hukumomi na samun labarai na yiwa 'yan mata fyade da ma wadanda ba a gama goyon su ba a Najeriya. Galibi tsofaffi da mata ne ake samun su da aikata wannan danyen aiki.

Har ma yara maza ba su tsira daga labarin yin luwadi da su ba, daga mutanen da ke kusa da su, ko kula da su a matsayin masu kai su makaranta ko koya mu su karatu.

Najeriya mai mutane kimanin miliyan 180 nada akasari mafi yawan jama'ar ta matasa, kuma yawancin jama'ar nada addini da al'adu amma duk da haka an samu karuwar bata gari da masu miyagun hali, lamarin da ya tilasta fidda hukuncin da ya dace da masu laifin.

Mairo Mudi ta kungiyar "Media For Morals" na daga mata da ke kamfen din kiran samu dokoki masu tsauri don yaki da fyade. Ta bukaci masu tsara dokoki su bullo da hukunci mai tsanani ga duk wanda a ka samu da laifin hakan, tace kar ya gaza daurin rai da rai koma kawar da irin su daga doron kasa.

A taron da su ka yi a Abuja majalisar tallafawa shugaba Buhari wajen tsara manufofi PSC, ta ce lauyoyinta na shirya kudurin doka mai tsanani kan wannan kalubalen.

Da alamu fitowar da matar mawakin nan Busola Timi Dakolo ta yi da zargin Pastor Biodun Fatoyinbo na Commonwealth of Zion, ya yi mata fyade tun tana karama, ya karfafawa mata da dama guiwa wajen bayyana irin wannan cin zarafi da a ka taba yi mu su.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Cin Zarafin Yara Ta Fyade Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya