A rahotannin da muke kawo muku na watan Ramadana, a yau dandalinVOA ya samu bakuncin likitar amosanin jini, Dr. Aisha Amal Galadanchi, da ke Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, wadda ta ce kasancewarta likitar masu wannan cutar, a watan Ramadan takan ba masu irin wannan lalurar shawarar cewa idan ciwon na yawan tsanantawa, kar su yi azumi a lokacin.
Ta ce ita cutar sikila, wato amosanin jini, ba ta son jikin mutum ya bushe, ko a dinga samun karancin ruwa, ko takura musamman ga wadanda suke yawan tashi wanda yake bukatar yawaitar shan magunguna.
Ta kara da cewa mafi yawan masu wannan ciwo da nasu yake yawan tashi musamman ganin cewar ciwon a wasu lokutan ba wuya jinin mutum ya kafe, ana ba shi shawarar sauwake wa kansa wannan azumi a lokacin.
Your browser doesn’t support HTML5